Kamfanin Dillancin labarai na IRINN ya rawaito yewa wani dan sanda a jahar salahuddin yace; ranar litinin yan ta'adda na kungiyar Da'ish sun sace mutane dayawa wadanda wasu daga cikin su ma'aikata ne da kuma yan gudun hijira ya zuwa yanzu ba a san inda suka kai suba.
Mai bada labarin wanda ya bukaci a sakaya sunann sa yace; kama yanzu yan ta'adda sun kashe mutane takwas daga cikin wadanda suka kama kuma daga cikin su a kwai jami'an yan sanda.
A bage daya, sojojin Iraki da na sa kai na cigaba da samun nasara awurare daban-daban wajan kwato yankunan da suke hannun yan ta'adda.ABNA